Wasu al’ummar Fulani Makiyaya da aka kora daga garin Igagan na jihar Oyo da ke kudancin Najeriya a bara, da yanzu haka ke gudun hijira a wasu wuraren na kukan neman taimako.
Makiyayan sun ce har yanzu suna cikin mawuyacin hali, kuma babu wani tallafi da aka kai masu.
Al’amarin dai ya tilasta wa da dama daga cikinsu komawa ga yin barace-barace, domin samun abinda za su ci.
A cikin watan Janairun shekarar da ta gabata ne aka kai wa Fulanin harin a rugagensu tare da kashe wasunsu da dabbobinsu da kona masu gidaje.
Aliyu Dan Sarkin Fulanin jihar Oyo, ya ce shekara guda bayan harin da aka kai wa Makiyayan, a Igangan dake karamar hukumar Ibarapa ta arewa a jihar Oyo, har yanzu rayuwarsu ta na cikin babbar matsala.
Ya ce har yanzu ba su da takamaimai wuri guda na zama, ‘ya’yansu ba sa zuwa makarantar boko, babu makarantar allo wasu kafin su samu abinci matsala ce, wasu ma tun da aka yi abin, ba a san inda suke ba.
Sana’o’in da muke yi a baya babu wadanda ba su da makwanci, amma a yanzu a masallaci mu ke kwana, wasu sai sun yi bara sannan suke samun abin kai wa bakin salati.