Gwamnatin tarayya ta bukaci kasar Saudiyya da ta dage takunkumin da ta sanya wa matafiya ‘yan Najeriya biyo bayan bullar nau’in Korona ta Omicron a kasar Afirka ta Kudu da aka gano a tsakanin wasu matafiya da aka ce sun ziyarci Najeriya.
Ambasada Zubairu Dada, Karamin Ministan Harkokin Waje ne ya yi wannan roko a ranar Asabar lokacin da ya gana da Jakadan Saudiyya a Najeriya Ambasada Faisal bin Ebraheem Al-Ghamdi, Channels TV ta rahoto.
Dada a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ibrahim Aliyu ya fitar, ya bukaci mahukuntan Saudiyya da su sake duba takunkumin hana zirga-zirgar da suka sanya wa ‘yan Najeriya dangane da bullar Omicron.
Ya bukaci Saudiyya da ta yi koyi da kasashe da dama da suka saka wa Najeriya takunkumi tun da farko sannan suka dage bayan dogon nazari.
Hakan na faruwa ne yayin da ya yi alkawarin ci gaba da baiwa jakadan goyon baya da hadin kai wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.
A nasa jawabin, Ambasada Al-Ghamdi ya bayyana jin dadinsa da kokarin da gwamnati ke yi na dakile yaduwar nau’in Omicron na Korona tare da yin alkawarin isar da sakon Najeriya ga hukumomin da abin ya shafa a gida Saudiyya.