Home Home Ta’aziyya: Gwamna Ganduje Ya Kai Ziyara Gidan Su Hanifa Abubakar

Ta’aziyya: Gwamna Ganduje Ya Kai Ziyara Gidan Su Hanifa Abubakar

142
0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa iyayen Hanifa Abubakar ta’aziyyar rasuwar ‘yarsu wacce malamin makarantarsu ya kashe bayan da ya yi garkuwa da ita.

Kwana 47 bayan sace dalibar tasa ‘yar shekara biyar, jami’an tsaro suka kama Abdulmalik Tanko a lokacin da ya je karbar kudin fansa.

Amma gabanin hakan malamin makarantar ta Noble Kids Academy, ya riga ya kashe Hanifa amma duk da haka yake karbar kudin fansa.

Ganduje ya ce sun sami tabbaci daga kotun da ke sauraren karar cewa za a yi adalci, inda ya sha alwashin ba zai bata lokaci ba wajen bin umarnin kotu da zarar an yake hukuncin kisa.

Ya ce duk wanda aka samu da laifi a wannan mummunan aika-aika, zai fuskanci hukuncin kisa ba tare da bata lokaci ba, a matsayinmu na gwamnati, tuni mun riga mun fara bin matakan da suka dace.

Gwamna Ganduje ya kuma yi alkawarin cewa gwamnati za ta kula da iyayen marigayiya Hanifa.