Home Labaru Rashin Tsaro: An Sace Surukar Shugaban Ma’aikata Da Wata Mata A Jihar...

Rashin Tsaro: An Sace Surukar Shugaban Ma’aikata Da Wata Mata A Jihar Neja

258
0

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da surukar shugaban ma’aikata na gwamnatin jihar Neja Alhaji Ibrahim Balarabe da wata mata a garin Kagara.

Daya matar dai ta kasance matar wani babban jami’in hukumar kiyaye hadurra ta kasa da ke zama a garin Kagara.

Wata majiya ta ce, ‘yan bindigar sun nemi iyalan wadanda aka sace su ba su kudin fansa, sai dai har yanzu ba a san ko nawa su ke nema ba.

Majiyar ta cigaba da cewa, ‘yan bindigar sun shiga garin Kagara ne da safiyar ranar Asabar da ta gabata, inda su ka yi harbe-harbe kafin su sace matan biyu.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Abubakar Muhammed, ya ce zai sake kiran mai daukar rahoto dangane da lamarin, amma bai bada tabbacin faruwar lamarin ba. ���.