Home Labaru Bidiyon Lai: Jam’iyyar PDP Ta Nemi Shugaba Buhari Ya Sauka Daga Kujerar...

Bidiyon Lai: Jam’iyyar PDP Ta Nemi Shugaba Buhari Ya Sauka Daga Kujerar Mulki

355
0
Lai Mohammed, Ministan Labarai Da Al’adu

Jam’iyyar PDP ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka daga kujerar mulki, sakamakon wani bidiyo da ministan yada labarai da al’adu Lai Mohammed ya yi, inda ya roki ‘yan Nijeriya su yafe wa shugaba Buhari a kan shahadar kammala makarantar sakandare.

PDP ta yi korafin cewa, bidiyon daidai ya ke da amsa laifin sa da kuma wani yunkuri na bada hakuri da son zuciya, ganin cewa Shugaba Buhari ya gaza kare kan sa a gaban kotun zaben Shugaban kasa.

Jam’iyyar PDP, ta ce ba abu ne mai muhimmanci ba cewa ko an kirkiri bidiyon ne ko kuma ministan ya yi jawabin ne a shekara ta 2015 kamar yadda aka yi ikirari.

Da ya ke jawabi a wajen wani taron manema labarai a Abuja, sakataren jam’iyyar PDP na kasa Kola Ologbodiyan, ya ce an baza bidiyon ne ga duniya domin ya taba zuciyar kotun zaben ta yadda za ta bi doka bayan an gabatar mata da kwakkwarar hujja a gaban ta.  

Ministan labarai da al’adu Lai Mohammed dai ya roki ‘yan Nijeriya su yafe wa shugaba Muhammadu Buhari, sakamakon  batar da takardun kammala makarantar sa na sakandare da ya yi.