Wani babban jami’in soji Manjo Janar Christopher Musa, ya ce rashin kyan hanyoyi da Nakiyoyin da ake dasawa ya na janyo masu tarnaƙi a yakin da su ke yi da ‘yan ta’adda.
Manjo Janar Christopher, ya ce sun cire nakiyoyi sama da
98 zuwa yanzu, kuma har yanzu ba su fidda ran samun
wasu ba.
Ya ce tsakanin Maiduguri zuwa Monguno a jihar Borno
tafiya ce mai nisan kilomita 180, amma sai an sauka an
gyara hanya ko saboda rashin kyawun hanya ta.
Manjo Janar Musa, ya bukaci gwamnati ta taimaka ta
gyara hanyoyin da su ka lalace don a ba sojoji damar
gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.
Babban jami’in sojin, ya ce akalla ‘yan ta’adda dubu 11
sun miƙa wuya bayan irin ayyukan da rundunar su ta yi a
yankin arewa maso gabashin Nijeriya.














































