Home Labarai An Kashe ‘Yar Shekara Biyar Da Wasu Su Ka Yi Garkuwa Da...

An Kashe ‘Yar Shekara Biyar Da Wasu Su Ka Yi Garkuwa Da Ita A Bauchi

138
0

Jami’an hukumar tsaro ta Civil Defence a Jihar Bauchi, sun kama wasu maza biyu bisa zargin yin garkuwa tare da kashe wata yarinya ‘yar shekaru biyar bayan karbar kudin fansa a hannun iyayen ta.

Yayin gabatar da wa]anda ake zargin ga manema labarai
a helkwatar hukumar da ke Bauchi, kwamandan jihar
Nuruddeen Abdullahi, ya ce mutanen sun yi garkuwa da
yarinyar ne a kofar gidan su, inda su ka tafi da ita karkashin
wata gada su ka shake ta, sannan su ka sanya ta cikin
buhu duk da cewa sun karbi kudin fansa.

Rahotanni sun ce, daya daga cikin wadanda su ka yi
garkuwa da yarinyar makwafcin iyayen ta ne.

Yarinyar mai suna Khadija, makwabcin su ya sace ta ne
lokacin da ta ke wasa a kofar gida, inda da farko ya nemi a
ba shi kudin fansa naira miliyan daya, amma daga bisani
aka tsaya a kan naira dubu 150.

Leave a Reply