Home Labaru Rashawa: Kotu Ta Sa 29 Ga Watan Afrilu Domin Fara Sauraran Karar...

Rashawa: Kotu Ta Sa 29 Ga Watan Afrilu Domin Fara Sauraran Karar Sambo Da Yuguda

398
0

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 29 ga
watan Afrilu don fara sauraron karar da aka shigar da Sambo
Dasuki da Bashir Yuguda a kan zargin satar naira biliyan 19 da
miliyan dari 4.
Wata majiya ta ruwaito cewa, sauran wadanda ake tuhumar
bayan Sambo Dasuki da Yuguda sun hada da tsohon gwamnan
jahar Sokoto Attahiru Dalhatu Bafarawa, dan sa Sagir da kuma
kamfanin sa na Dalhatu Investment Limited.
Hukumar EFCC na tuhumar mutanen ne a kan aikata laifuka 25,
wanda hakan ya sa Alkali Hussein Baba Yusuf ya dage sauraran
karar bayan jin korafe-korafen Alkalan wadanda ake kara.
Da fari dai, lauyan EFCC, Oluwaleke Atolagbe ya bayyana
cewa, sun yi iya bakin kokarin su wajen ganin hukumar DSS da
ke rike da Dasuki ta gabatar da shi a gaban kotu, amma hukumar
ta ce, Dasuki da kan sa ne yaki amincewa ya halarci zaman
kotun.
Shi kuwa lauyan Bafarawa, Lateef Fagbemi ya bayyana
damuwar sa ne a gaban kotun, game da yadda shari’ar ke tafiyar
hawainiya, inda ya ce a karshen makonnan shari’ar ke cika
shekaru hudu ana ta fafatawa, don haka ya ce idan EFCC ba zata
iya ba ta janye karar kowa ya huta.