Home Labaru Rantsar Da Macky Sall: Shugaba Buhari Ya Dawo Gida Nijeriya Daga Kasar...

Rantsar Da Macky Sall: Shugaba Buhari Ya Dawo Gida Nijeriya Daga Kasar Senegal

220
0

Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo gida Nijeriya bayan ya
halarci taron bikin rantsar da shugaban kasan Senegal Macky
Sall karo na biyu bayan ya sake lashe zaben ya yi a kasar.
Daga cikin shugabannin kasashen Afrika da suka halarci taron
sun hada da shugaban kasar Nijar Mohammadou Issoufou da
shugaban kasar Ivory Coast Alhassan Watara da shugaban kasar
Gabon Adama Barrow da shugaban kasar Ruwanda Paul
Kagame da dai sauran su.
Taron wanda aka gudanar a Dakar babbar birnin kasar a ranar
Talatar da ta gabata, ya samu halartar wasu daga cikin tsaffin
shugabanin da suka hada da Olusegun Obasanjo da shugaban
bankin cigaban Afrika Akinwumi Adesina da shugaba Sahara
Power Group Kola Adesina da shugaban bankin UBA Tony
Elumelu.
Idan dai na a manta ba, shugaba Buhari ya isa birnin Dakar ne ,
a daren ranar Litinin din da ta gabata, sakamakon gayyatar sa da
aka yi a matsayin babban bako na musamman a bikin rantsarwa.