Home Labaru Tsaro: Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi Ta Kaddamar Da Rundunar Puff Adder

Tsaro: Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi Ta Kaddamar Da Rundunar Puff Adder

221
0

A kalla masu laifi 39 rundunar yan sandan jihar Bauchi ta kama jim kadan bayan kaddamar da rundunar Puff Adder domin dakile aiyukan masha’a da ke fama da su a jihar.

Da yake gabatar da jawabi a lokacin kaddamar da rundunar, kwamishinan ‘yan sandan jihar Ali Aji Janga ya ce sun kaddamar da rundunar ne domin yin biyayya ga umarnin babban sifeton ‘yan sandan Nijeriya Muhammad Abubakar.

Janga ya bayyana hakan ne a hedikwatar rundunar ‘yan sandan da ke Bauchi a yayin da ake gabatar da masu laifin su 39 da suka hada da masu satar mutane da kuam ‘yan fashi da mukami.

Idan dai ba a manta ba, babban sufeton ‘yan Nijeriya muhammad Abubakar ya kaddamar da rundunar Puff Adder ne domin kawo karshen matsalar tsaro a sassan Nijeriya, musamman matsalar garkuwa da mutane a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Daga cikin makaman da aka kwato a hannun masu laifin, akwai bindigar baushe 5 da adduna guda 9 da sharbebiyar wuka 1babura uku da kuma tulin tabar wiwi.