Home Labaru Rangwame: Amurka Ta Yi Doka A Kan Farashin Magunguna

Rangwame: Amurka Ta Yi Doka A Kan Farashin Magunguna

164
0

Shugaba Trump na kasar Amurka, ya sa hannu a kan wasu dokoki huɗu da za su bada damar rage farashin magunguna ga ‘yan ƙasar.

Ɗaya daga cikin dokokin za ta bada damar yin odar maguguna a farashi mai rahusa daga wasu ƙasashe kamar Canada, yayin da wata dokar ta yi tanadin zaftare wasu kuɗaɗe a matsayin rangwame ga masu saye.

Donald Trump, ya ce matakin zai taimaka wa Amurkawa wajen samun magunguna ba tare da wata wahala ba.