Home Labaru Cutar Korona: Za A Rufe Duk Wata Mashaya Da Gidan Rawa A...

Cutar Korona: Za A Rufe Duk Wata Mashaya Da Gidan Rawa A Catalonia

156
0
Coronavirus: Matakan Da Najeriya Ta Dauka Ta Dauka
Coronavirus: Matakan Da Najeriya Ta Dauka Ta Dauka

Gwamnatin yankin Catalonia da ke arewa maso gabashin Sifaniya, ta bada umarnin rufe duk wani gidan rawa da wata mashaya da ke aiki da dare a yankin har zuwa wa’adin makonni biyu.

Gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne sakamakon ƙara samun adadi mai yawa da ke kamuwa da cutar korona

Kusan wata ɗaya bayan Sifaniya ta kawo ƙarshen dokar ko-ta-kwana da ta sanya, manyan garuruwa irin su Barcelona da Zaragoza da kuma Madrid babban birnin ƙasar na ganin ƙaruwa a yawan masu kamuwa da cutar.

Ma’aikatar lafiya ta Sifaniya ta bada rahoton cewa, sama da mutane 900 su ka kamu da cutar a ranar Juma’ar da ta gabata.

Tuni Faransa ta gargaɗi ‘yan ƙasar ta kan cewa kada su kuskura su je yankin Catalonia, yayin da ƙasar Norway ta ce za ta fara killace duk wanda ya isa ƙasar daga Sifaniya.