Home Labaru Ranar ‘Yanci: Kada Mazauna Abuja Su Razana Idan Sun Ji Rugugin Bindigogi...

Ranar ‘Yanci: Kada Mazauna Abuja Su Razana Idan Sun Ji Rugugin Bindigogi – Sojoji

354
0

Rundunar Sojin Nijeriya, ta fitar da sanarwar da ke cewa kada mazauna yankin Abuja su firgita idan su ka ji karar harbin bindigogi na tashi a ranar 1 ga watan Oktoba.

Wannan dai rana ce da Nijeriya ke cika shekaru 59 da samun ‘yanci, kuma an shirya sojoji za su yi wa Shugaban kasa faretin ban-girma a Fadar sa da ke Abuja.

Faretin, wanda sojojin Guards Brigade za su yi, an bukaci musamman mazauna unguwannin Asokoro da Maitama da kewayen Fadar Shugaban Kasa cewa, idan sun ji rugugin tashin bindigogi kada su razana.

Mataimakin Kakakin Yada Labarai na rundunar Soji Haruna Tagwai ne ya fitar da wannan sanarwa, inda ya ce za a harba bindigogin ‘artillery’, kuma kada mutane su firgita.