Home Labaru Harkallar Fansho: Kotu Ta Bukaci A Wallafa Kadarorin Da Aka Karbe Wa...

Harkallar Fansho: Kotu Ta Bukaci A Wallafa Kadarorin Da Aka Karbe Wa Maina

237
0
Abdulrasheed Maina, Tsohon Shugaban Hukumar Fansho
Abdulrasheed Maina, Tsohon Shugaban Hukumar Fansho

Babban kotun tarayya da ke zama a Legas, ta yanke hukunci game da shari’ar da ake yi tsakanin wani Lauya da gwamnatin Nijeriya game da binciken Abdulrasheed Maina da ake yi.

Wata majiya ta ce, Alkalin kotun ya nemi a fito da sunayen duk kadarorin da aka karbe daga hannun AbdulRasheed Maina.

Kotun, ta kuma umarci Ministan shari’a Abubakar Malami da hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC su bi wannan umarni.

Mai shari’a Oluremi Oguntoyinbo, ta ce gwamnati ta wallafa jerin duk wasu kadarori da dukiyoyin Maina da aka karbe a binciken da ake yi ma shi.

Wata kungiya mai zaman kan ta “Centre for Law and Civil Culture” a Turance, ta nemi kotu ta umarci gwamnatin tarayya ta hannun ofishin babban Lauyan gwamnati da hukumar EFCC su bayyana kadarorin da aka karbe a wajen Maina.