Home Labaru Ranar Murna: Jiga-Jigan PDP Sun Halarci Daurin Auren ‘Ya’yan Atiku A Kaduna

Ranar Murna: Jiga-Jigan PDP Sun Halarci Daurin Auren ‘Ya’yan Atiku A Kaduna

830
0

Manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP sun dira garin Kaduna domin halartar daurin auren ‘ya’yan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, wanda aka yi a masallacin Sultan Bello da ke Unguwar Sarkin musulmi a Kaduna.

An dai gudanar da daurin auren ne a ranar Asabar, 14 ga watan Disamba na shekara ta 2019 kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Daga cikin mahalarta daurin auren kuwa akwai Gwamnan jihar Adamawa Umaru Fintiri da tsohon gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo, da tsohon gwamnan jihar Bauchi Ahmed Adamu Mu’azu, da tsohon gwamnan jihar Kaduna Mukhtar Ramalan Yero.

Sauran sun hada da shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar  PDP Walid Jibril, da Farfesa Ango Abdullahi, da tsohon shugaban jam’iyyar PDP na rikon kwarya Ahmed Muhammad Makarfi, da tsohon shugaban hkumar EFCC Mallam Nuhu Ribadu, da Ambasada Ibrahim Kazaure, da Sanata Muhammad Tsauri da sauran manyan mutane.