Home Labaru Kiwon Lafiya An Nada Uwargidan Osinbajo Shugabar Kwamitin Yaki Da Cutar Tarin Fuka

An Nada Uwargidan Osinbajo Shugabar Kwamitin Yaki Da Cutar Tarin Fuka

670
0
Dolapo Osinbajo, Uwar Gidan Mataimakin Shugaban Kasa
Dolapo Osinbajo, Uwar Gidan Mataimakin Shugaban Kasa

Uwargidan shugaban kasa A’isha Buhari, ta nada mai dakin mataimakin shugaban kasa Dolapo Osinbajo a matsayin jagoran kwamitin yaki da cutar tarin fuka.

Babban sakataren Kungiyar Yaki da Tarin Fuka ta Nijeriya Mayowa Joel ya sanar da haka a wajen taron kungiyar da ya gudana a Abuja.

Tarin fuka dai cuta ce da ake kamuwa da ita ta hanyar shakar kwayar cutar, lamarin da ya sa A’isha ta bukaci kungiyar matan gwamnoni su hada hannu da masu ruwa da tsaki domin dakile yaduwar ta a Nijeriya.

Ta ce Matan gwamnoni na da mahimmiyar rawar da za su taka wajen ganin ‘yan Nijeriya sun yi bankwana da wannan cuta.

Binciken ya nuna cewa, a duk shekara mutane dubu 407 ke kamuwa da wannan cuta a Nijeriya, sannan daga cikin su kashi 25 cikin 100 ke samun maganin cutar.

Nijeriya ta fada cikin matsalar ne, sakamakon rashin gyara cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko da rashin samar da isassun magunguna da rashin kwararrun ma’aikata da kuma rashin kayan aiki.

Leave a Reply