Home Labaru Neman Fansa: APC Ta Bukaci Gwamnati Ta Kwace Kamfanonin MTN Da Shoprite...

Neman Fansa: APC Ta Bukaci Gwamnati Ta Kwace Kamfanonin MTN Da Shoprite Da DSTV

299
0

Jam’iyyar APC ta bukaci gwamnatin tarayya ta tabbatar ‘yan Nijeriya sun mallaki kamfanoni da masana’antu mallakar kasar Afrika ta Kudu da ke Nijeriya.

Manyan kamfanonin Afrika ta Kudu da ke Nijeriya dai sun hada da kamfanin sadarwa na MTN, da kamfanin tashohin tauraro na DSTV, da babban shagon cinikayya na ‘Shoprite’ da sauran su.

Jam’iyyar, ta kuma bukaci gwamnatin Nijeriya ta kwace lasisin duk wasu bankuna mallakar ‘yan kasuwar kasar Afrika ta Kudu da ke aiki a Najeriya, wadanda su ka hada da Bankin Stanbic IBTC, da Bankin Standard Chartered.

Yanzu haka dai kamfanonin MTN da DSTV sun bada umarnin rufe ofisoshin su da ke manyan biranen Nijeriya, biyo bayan fara kai masu hare-haren daukar fansa sakamakon harin da ‘yan Afrika ta Kudu ke ci-gaba da kai wa ‘yan Nijeriya da wuraren kasuwancin su a can.