Home Labaru Nasarorin Da Na Samu A Zamfara – Gwamna Matawalle

Nasarorin Da Na Samu A Zamfara – Gwamna Matawalle

1201
0

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya yi wa shugaban kasa Muhammad Buhari jawabi a kan nasarar da ya samu wurin kawo karshen rikicin ‘yan bindiga a jihar.

Gwamnan ya gana da shugaban kasa ne a gidansa dake Daura, inda kuma bayan sun kammala ganawar ya zanta da manema labarai akan abinda suka tattauna.

Matawalle,  ya ce a cikin watanni biyu kacal a ka sami nasara akan yan ‘ta’adda a jihar, ya tabbatar da cewa aiki yanzu aka fara.

Ya kara da cewa a yanzu akwai kwanciyar hankali da zaman lafiya a Zamfara, wannan kuma wani abu ne da shekarun baya jihar Zamfara ta rasa.  

Ya kara da cewar al’ummar Hausawa da Fulani na zama tare lami lafiya, kuma a kullum gwamnati kira ta ke ga jama’ar ta akan sanin muhimmancin zaman lafiya.  

Ya ce gwamnati ta sulhunta ‘yan bindiga da sauran al’ummomin da rikicin ya shafa ba tare da ba su kudi ba, wanda  hakan ya sa duk wadanda aka kama yanzu an sako su ba tare da biyan fansar ko kwabo ba.