Gwamnatin Jihar Zamfara ta kaddamar da shirin raba kayan abincin azumi da na Sallah ga marayu 40,000.
Shugaban Hukumar Zakka ta Jihar Zamfara Bashir Sirajo, ya ce an zabo marayu dubu 1 da 800 daga kowace Masarauta daga cikin Masarautu 16, yayin da aka zabo marayu 3,600 a Masarautar Gusau.
Ya ce za a raba wa kowannen su kayan abinci da su ka hada da shinkafa, da sukari, da wake da kuma yadi da kudin dinki.
Dangane da yawan abincin da za a raba kuwa, Sirajo ya ce kowace masarauta za a ba marayun kayan abinci cikin mota biyu da rabi.
Gwamna Abdulaziz Yari, ya gargadi jami’an da aka dora wa nauyin rabon kayan abincin su yi adalci, domin amana ce aka damka masu.
Ya kuma yi kira ga jama’a su cigaba da addu’ar kawo karshen fitinar da Jihar Zamfara ke fama da ita.
You must log in to post a comment.