Home Labaru Batanci: Obasanjo Ya Maka Jaridar The Punch Kotu

Batanci: Obasanjo Ya Maka Jaridar The Punch Kotu

395
0

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya maka jaridar THE PUNCH kotu, tare da neman diyya bisa bata ma shi suna da zubar masa da mutunci da jaridar ta yi.

Obasanjo dai ya na neman diyyar ne a kan jaridar da wani fitaccen marubucin ta mai rubutu mako-mako Sola Olumhense, inda ya nemi a biya shi naira biliyan daya saboda da munin cin mutuncin da ya ce an yi ma shi.

Obasanjo ya kai karar ne a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, dangane da rubutun da Sola Olumhense ya yi a kan sa ranar 17 ga watan Janairu na shekara ta 2019.

Ya ce Jaridar ta buga karairayin da Sola Olumhensen ya rubuta a kan sa, wadanda babu gaskiya a ciki kuma babu hujjoji, sannan cin mutunci ne da zubar ma shi da girma ne, kuma sun janyo jama’a na gudun shi tare da tozarta shi.

A cikin rubutun dai Olumhense ya ce, Obasanjo na nuna wa duniya cewa shi mutumin kirki ne, amma ba haka ya ke ba, sannan ya kafa hukumomin EFCC da ICPC ne don su zame ma shi karnukan farautar wadanda ba su shan inuwa daya da shi.

Leave a Reply