Home Labaru Lafiya: Takaddama Tsakanin Gwamnatin Neja Da Kamfanonin Da Ke Kula Da Shirin...

Lafiya: Takaddama Tsakanin Gwamnatin Neja Da Kamfanonin Da Ke Kula Da Shirin Inshora

294
0

Gwamnatin jihar Neja, ta ce daga yanzu ba za ta sake yin amfani da kamfanonin da ke biyan asibitocin da ke karkashin shirin inshorar Lafiya a sabon tsarin inshorar kiwon lafiya ta jihar ba.

Jami’in ma’aikatar lafiya ta jihar Makusidi M.M. ya sanar da haka a Minna.

Makusidi ya ce, gwamnati ta yanke hukuncin ne saboda rashin biyan asibitocin da ke karkashin shirin inshorar lafiya da kamfanonin ke yi.

Ya ce tun da aka kafa shirin inshorar lafiya ta kasa, kamfanonin sun karbi akalla Naira biliyan 350, amma duk da haka mutane kalilan ne ke cikin tsarin kuma ba su samun kula yadda ya kamata, lamarin da ya sa mutane musamman talakawa ba su amfana da shirin yadda ya kamata.

A karshe ya ce babban burin gwamnatin jihar shi ne, ta ga mutane musamman talakawa su na samun kiwon lafiya kamar kowa.

Leave a Reply