Home Addini Ramadan: Yobe Ta Ware n103m Don Ciyarwa Da Wa’Azi

Ramadan: Yobe Ta Ware n103m Don Ciyarwa Da Wa’Azi

310
0

Gwamnatin jihar Yobe, ta ware Naira miliyan 103 domin
ciyar da marasa galihu da kula da malamai masu wa’azi a
watan Ramadan.

Da ya ke zantawa da manema labarai a Damaturu, Kwamishinan Harkokin addini Alhaji Mala Musty, ya ce
Gwamna Buni ya amince da kashe Naira miliyan 73 domin sayen raguna da kayan dafa abinci a cibiyoyin ciyar da abinci 67 da aka samar a jihar.

Haka kuma, an ware Naira miliyan 30 domin biyan alawus ga malamai masu wa’azin Ramadan na wannan shekarar.

Ya ce tun kafin zuwan Gwamna Buni al’adar gwamnatin Jihar Yobe ce ciyar da mabukata a watan Ramadan da sunan Iftar.

Alhaji Mala Musty ya kara da cewa, gwamnati ta ware buhunnan shinkafa dubu 1 50 domin ciyarwa har zuwa karshen watan Ramadan.

Leave a Reply