Home Labarai Kungiyoyin Arewa Sun Yi Fatali Da Bukatar Sakin Nnamdi Kanu

Kungiyoyin Arewa Sun Yi Fatali Da Bukatar Sakin Nnamdi Kanu

67
0

Gamayyar Kungiyoyin Arewa, sun yi fatali da kiraye-kirayen
a saki shugaban haramtacciyar kungiyar masu rajin kafa kasar
Biafra Nnamdi Kanu.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Kakakin kungiyar Abdul- Azeez Suleiman, ya ce kiraye-kirayen a saki Nnamdi Kanu ba tare da shari’a ba da shugabanni da kungiyoyin Ndigbo su ka yi ta kara kamari ne tun bayan zaben shugaban kasa.

Kungiyar ta yi nuni da cewa, kungiyoyi irin su Ohanaeze Ndigbo sun shiga cikin yakin zagon kasa, ta hanyar amfani da sakin Nnamdi Kanu a matsayin wani sharadin hadin gwiwa da Ndigbo da gwamnatin Tinubu.

Don haka kungiyar ta yi Allah-wadai da sabbin kiraye-kirayen a dakatar da shari’ar Nnamdi Kanu da kungiyar Ohanaeze da sauran shugabanni da kungiyoyin Ndigbo suka yi, inda ta bayyana shi a matsayin rashin hankali da rashin sanin ya kamata da rashin tunani.

A karshe ta yi kira ga hukumomin tarayya su yi watsi da irin wadannan kiraye-kirayen, su kuma jajirce wajen ganin an gurfanar da Nnamdi Kanu a gaban shari’a don kada a kafa wani mummunan misali na yadda shugabannin yankin ke tsoma baki a lamarin.

Leave a Reply