Home Labaru Ruga: Ba Mu Amince Fulani Su Da Wo Arewa Ba -Inyamurai

Ruga: Ba Mu Amince Fulani Su Da Wo Arewa Ba -Inyamurai

276
0

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje tare da shugabannin Iyamurai na Kano, sun ce ba su amince da cewar Fulani su bar Kuduncin Najeriya su dawo Arewa ba.

Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano
Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano

Sakateran yada labaran na  Kano Abba Anwar, ya ce shugabaninn Inyamuran wadanda suka hada da Eze Ndigbo da kuma Boniface Igbokwe suka bayyana haka a lokacin wata liyafa da gwamnan ya shirya a Kano.

Shugabaninn sun ce ba su amince da wadanda ke cewa Fulani Makiyaya  su bar Kudu ba, saboda  duk ‘dan Najeriya nada yancin zama a inda ya ga dama a Nigeria.

Shi ma a lokacin da yake magana gwamna Abdullahi Ganduje, ya ce Nijeriya kasa ce mai addinai daban-daban, ya na da kyau mutane su girmama banbance banbancen dake tsakaninsu.

Ganduje, ya kara da cewar saboda haka ya ke kira ga gwamnatin tarayya ta kawo karshen yawon makiyaya daga gari zuwa gari, domin  babbar matsalar makiyaya shi ne rashin ilimi kuma ya faru ne ta dalilin rashin zamansu a waje daya.

Gwamnan jihar Kano, ya ce shiyasa gwamnatinsa  ta kaddamar da kwamitin samar da RUGA domin bunkasa tattalin arziki a jihar Kano tare da magance fitinar da take faruwa tsakanin manoma da makiyaya.