Home Labaru Rage Jam’iyu: INEC Ta Garzaya Kotun Koli

Rage Jam’iyu: INEC Ta Garzaya Kotun Koli

502
0
Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta kasa, INEC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta Kasa, INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC tace zata kalubalanci hukuncin kotun Daukaka kara cewa ta dawo da Jam’iyar ACD da wasu 22 da hukumar ta soke rijistar su.

Kwamishinan wayar da kan jama’a kan kada kuri’a Festus Okoye yace a ranar 29 ga watan Yunin shekarar 2020 ne kotun daukaka kara dake Abuja, a karar da Jam’iyar NUP ta shigar, ta tabbatar wa hukumar hurumin soke Rijistar duk jam’iyar dab a ta cika ka’idojinsashe nan 225 A na kundin tsarin mulki ba .

Jam’iyar NUP ta daukaka kara wanda har yanzu hukuncin na gaban kotun koli.

Okoye yace yanzu haka hukumar zaben na fuskantar hukunci biyu maus karo da juna daga kotun daukakakara. Daya ya tabbatar wa hukumar Ikon soke Jam’iyun, na biyun kuma ya haramta soke jam’iyyun 22 sa kuma ACD daga jerin Jam’iyyun kasar nan.

To sai dai yace yanzu hanakalin hukumar ya karkata ne wurin tsare-tsaren yadda za’a gudanar da zabukan jahohin  Edo da kuma Ondo a ranakun 19 ga watan satumba da kuma 10 ga watan Oktoba.

Leave a Reply