Gwamnatin tarayya ta Umurci ma’aiakatan dake mataki na 12 zuwa 13 da wadanda suke ayyukan da suka zamo dole su fara zuwa aikikullun.
Shugaban ma’aiakata ta kasa Folashade Yemi-Esan, ta bayar da Umurnin a jiya Litinin 10 ga watan Augustan shekarar 2020.
Shugabar tace wadanda zasu dawo aikin zasu rika zuwa aikin ne daga karfe 8:00 na safe zuwa karfe 4 na yamma a ranakun Litinin zuwa Juma’a.
Wannan mataki ya biyo bayan sanarwar ma’aiakatan dake mataki na 14 zuwa sama ne kadai ke zuwa aiki sau uku a makodomin kaucewa yaduwar cutar Covid-19.
Ta kuma Umurci manyan sakatarori da shugabannin ma’aiakatun Gwamnati su maido da ma’aiakatan dake gudanar da tilas bakin aiakin su
Daga karshe ta bukaci ma’aiakatan das u kasanace masu bin ka’idojin hana kamuwa da cutar, da suka hada da bada tazara da wanke hannu da kuma saka amawali.
You must log in to post a comment.