Home Labaru Ilimi Bude Makarantu: Hukumar NECO Ta Fitar Da Jadawalin Jarabawar Bana

Bude Makarantu: Hukumar NECO Ta Fitar Da Jadawalin Jarabawar Bana

464
0
NECO

Hukumar shirya Jarabawar kammalla makarantar Sakandare ta kasa NECO ta Fitar da jadawalin jarabawar shekarar 2020 ga dukkan Daliban da zasu zana jarabawar a bana.

Shugaban hukumar Farfesa Godswill Obioma ne ya kaddamar da jadawalin a ranar Talatan nan, inda yace za’a gudanar da jarabawar ne daga ranar 5 ga watan Oktoba mai zuwa zuwa 18 ga watan Nuwambar shekarar 2020.

Yace za’a gudanar da jarabawar kammalla karamar sakandare daga ranar 24 ga watan Augusta zuwa 7 ga watan satumbar shekarar 2020.

Ya kara da cewa daliban da zasu kammalla makarantun Primary zasu rubuta jarabawar su a ranar 17 ga watan Nuwanba.

Farfesa Obioma ya ce zuwa yanzu 169,144 ne suka yi rajistar jarrabawar ta NECO a sassan kasar nan. Daga karshe shugaban hukumar ya shawarci wadanda zasu zauna jarabawar NECO das u nemi tareda sauke Jadawalin a adireshin yanar Gizon hukumar wato www.neco.gov.com