Home Labaru Rage Cinkoson Gidan Yari: Gwamna Ganduje Ya Yi Wa Matar Da Ta...

Rage Cinkoson Gidan Yari: Gwamna Ganduje Ya Yi Wa Matar Da Ta Kashe Mijinta Afuwa

71
0
Teenager who killed husband freed

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wa wata mata da aka daure a gidan gyaran hali na jihar bayan samun ta da lafin kisan mijin ta afuwa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gidajen yarin jihar DSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa ya aike wa BBC Hausa, Gwamna Ganduje ya bayar da umarnin sakin Rahma Usaini da wasu mutum 30 da ke daure a gidan yarin jihar ta Kano.

Ya ce gwamnan ya dauki matakin ne bayan ganawa da kwamitin shugaban kasa kan rage cinkoson gidajen yari karkashin jagorancin Mai Shari’a Ishaq U. Bello.

An saki Rahma Usaini, mai shekara 20, wacce aka samu da lafin kisan mijinta Tijjani Muhammad a shekarar 2015, bayan ta shekara shida a gidan gyaran hali.

Rahotanni sun ce iyayen Rahma, mai shekara 13 a wancan lokacin, auren dole suka yi mata da Tijjani Muhammad.

Kwamitin ya kuma biya tara ta fursunonin da aka bai wa zabin biyan tara da wadanda suke cikin matsanaciyar rashin lafiya da kuma tsofaffi.