Home Labaru Dokar Tadi: Mahukunta A Rano Ta Jihar Kano Sun Haramta Zancen Dare

Dokar Tadi: Mahukunta A Rano Ta Jihar Kano Sun Haramta Zancen Dare

38
0
Dokar Dadi A Jihar Kano

Mahukuntan karamar hukumar Rano da ke Jihar Kano sun bijiro da wata sabuwar doka da za ta hana zance ko hirar dare tsakanin mata da maza matasa har da zawarawa.

Mahukuntan sun ce sun sanya wannan doka tsakanin masu neman aure a faɗin yankin da zummar kawo tsafta tsakanin matasa.

Wata sanarwa da shugaban karamar hukumar Dahiru Muhammed Ruwan Kanya,  ya fitar ya ce an dauki matakin ne ganin yada cikin shege ya yawaita da gurbata tarbiyya tsakanin masu zance da sunan neman aure.

Shugaban ƙaramar hukumar Ranon, ya shaida cewa lalacewar tarbiyya ce dalilin bijiro da wannan doka, don haka ya zame musu dole domin tabbatar da kyakkyawan tarbiyya tsakanin matasa da zawarawa a wannan zamanin.

Wannan mataki dai ya haifar da mabambanta ra’ayi ko da yake galibin iyayen yara da wasu matasa na ganin hakan ya dace.