Home Labaru Gwamnan Yobe Ya Bada Motocin Da Kujerun Makkah Ga Mahaddata Al-Qur’ani

Gwamnan Yobe Ya Bada Motocin Da Kujerun Makkah Ga Mahaddata Al-Qur’ani

478
0
Mala Buni , Gwamnan Jihar Yobe
Mala Buni , Gwamnan Jihar Yobe

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bada kyautukan motocin alfarma da guraben aikin Hajji ga mahaddatan da suka yi zarra a gasar haddar Al-Qur’ani ta jihar, wanda hukumar ilimin larabci da ilimin addinin musulunci ta jihar NBAIS ta shirya.

Rahotanni sun ambato mahaddata wadanda suka fito daga kananan hukumomin jihar 17 sun fafata a gasar, yayin da zakaran gasar zai wakilci jihar a babban gasar haddar Al-Qur’ani ta kasa da kasa da za’a yi a jihar Legas.

Alaramma Maina Muhammad daga karamar hukumar Machina shi ya lashe gasar a fannin haddar izihi 60 tare da Tajwidi a bangaran maza, yayin da malam Halima daga karamar hukumar Damaturu ta zamo ta daya a bangaren haddar Mata.

A kan wanna kokari ne Gwamna Buni ya ba kowanne daga cikin su kyautar sabuwar mota fil kirar Toyota, da kuma kujerar aikin Hajji, kamar yadda mataimakin gwamnan Idi Gubana ya bayyana wajen taron.

Gwamnan ya kuma yi kira ga Musulmai su kasance masu zuba jari wajen daukaka kalmar Allah ta hanyar kyautatawa tare da taimaka wa jama’a.

Haka kuma, gwamnan ya bukaci mahaddatan su dage wajen kare kambun jihar a babban gasar d ake kara karatowa domin su samu daman wakiltar Nijeriya a matakin kasa da kasa.