Home Labaru Yan Bindiga Sun Koma Amfani Da Na’Urar Sadarwa Ta Oba-Oba A Katsina

Yan Bindiga Sun Koma Amfani Da Na’Urar Sadarwa Ta Oba-Oba A Katsina

135
0

Sakataren gwamnatin jihar Katsina Mustapha Inuwa, ya ce yanzu ‘yan bindiga sun koma amfani da na’urar Oba-Oba wajen sadar da sakonni a tsakanin su.

Mustapha Inuwa, ya ce tun da gwamnati ta surfafi ‘yan bindiga, sai su ka koma tare hanyoyi da masu babura su na kwace man fetur daga tankunan su, tare da afka wa kauyuka su na kwace da fashin abinci da kayan sawa.

Ya ce yanzu kuma sun tsiro da sayen na’urar Oba-Oba domin isar da sakonni a tsakanin su, lamarin da ya ce babban koma-baya ne ga kokarin da ake yi na kawo karshen su a jihar Katsina da ma yankin Arewa Maso Yamma.

Mustaha Inuwa, ya ce duk da haka gwamnati ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen farautar ‘yan bindigar da ke amfani da na’urar ta Oba-Oba.

Leave a Reply