Gwamnatin jihar Bauchi ta sanya dokar ta baci a wasu yankuna na jihar bayan wani rikici da ya kaure tsakanin matasa a jihar.
A wata sanarwa wacce sakataren gwamnatin jihar, Mohammed Nadada Umar ya sanyawa hannu, ya bayyana cewa gwamnatin ta sanya dokar ne bayan rikicin da ya kaure tsakanin wasu matasa ranar Alhamis din nan.
Sanarwar ta bayyana cewa, matasan sun samu sabani da misalin karfe 9 na safe a karamar hukumar Gudum da ke jihar Bauchi, yayin da sabanin ya yi sanadiyyar tada rikici tsakanin matasan Gudum Sayawa da kuma matasan Gudum Hausawa.
Sanarwar ta kara da cewa, matasan sun tada rikici sosai, inda hukumomin tsaro suka shiga tsakani suka kwantar da tarzomar a yankin.
Sakataren gwamnatin jihar ya ce a lokacin da ake gabatar da sallar Juma’a rikicin ya kara tashi, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku.
Sanarwar ta bayyana cewa, ta sanya dokar ta bacin ne domin kawo karshen rikicin a yankunan, inda dokar za ta fara aiki da misalin karfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma. An bukaci al’ummar yankunan da abin ya shafa da su bi doka.
You must log in to post a comment.