Home Labaru Buhari Ya Zayyana Alheran Da Rufe Iyakokin Nijeriya Ya Haifar

Buhari Ya Zayyana Alheran Da Rufe Iyakokin Nijeriya Ya Haifar

344
0
Buhari Ya Zayyana Alheran Da Rufe Iyakokin Nijeriya Ya Haifar
Buhari Ya Zayyana Alheran Da Rufe Iyakokin Nijeriya Ya Haifar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce rufe iyakokin tudu da aka yi ya zama abin farin ciki ga manoman Nijeriya.

Buhari ya bayyana haka ne, a wajen wani taron da ya yi da wasu ‘yan Nijeriya a kasar  Ingila, inda ya ce rufe iyakokin Nijeriya ya taimaka wajen rage shigo da amfanin gona da makamai daga kasashen ketare.

Ya kuma jaddada cewa, Nijeriya ba ta rufe iyakokin ta domin ta muzguna wa makwaftan ta ba, sai don a karfafa tsaro da tattalin arzikin ta.

Shugaba Buhari, ya danganta rufe iyakokin da ci-gaban da aka samu ta fannin abinci a damina uku da su ka gabata, da kuma rage farashin taki da gwamnatin tarayya ta yi zuwa kashi 50.

Shugaban kasar ya jinjinawa ‘yan Najeriya da ke kasashen ketare a kan rawar da suke takawa fannoni da dama na kwarewarsu.

Yayin da ya ke bayanin a kan nasarorin da aka samu a bangaren habbaka tattalin arziki, da yaki da rashawa da kuma samar da tsaro, Buhari ya ce a kullum ana karfafa gwiwar matasan Nijeriya su koma gona domin ci-gaba da rayuwa mai tsafta tare da mutunta kawunan su.