Home Labaru Matsalar Tsaro: Masari Ya Bukaci Tallafin Gwamnatin Tarayya

Matsalar Tsaro: Masari Ya Bukaci Tallafin Gwamnatin Tarayya

298
0
Aminu Bello Masari, Gwamnan Jihar Katsina
Aminu Bello Masari, Gwamnan Jihar Katsina

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya bukaci gwamnatin tarayya ta samar da kudaden da za a tallafa wa mutanen da rikicin ‘yan bindiga ya rutsa da su a jihohin Sokoto da Zamfara da kuma Katsina.

Masari ya yi rokon ne, a wajen taron jin ra’ayoyin al’umma na kwana daya da Ma’aikatar Sadarwa ta Tarayya ta yi dangane da tsaro a Katsina.

Gwamna Masari, ya ce ya na bukatar gwamnatin tarayya ta ware wani tallafi na musamman, domin taimaka wa mutanen da rikicin ‘yan bindiga ya shafa a jihohin Arewa maso Yammacin Nijeriya uku.

Ya ce idan gwamnatin ta amince, za a yi amfani da kudin ne wajen samar da muhalli da sauran kayayyakin inganta rayuwa ga wadanda rikicin ya shafa, sannan a yi amfani da wani kaso domin biyan jami’an tsaro a jihohin uku.

Masari ya kara da cewa, gwamnatocin jihohin Katsina da Sokoto da Zamfara su na bukatar taimakon kudi domin taimaka wa mutanen da rikicin ya rutsa da su.