Home Coronavirus Ba Za Mu Yarda A Zaftare Albashin Ma’aikata Ba – NLC

Ba Za Mu Yarda A Zaftare Albashin Ma’aikata Ba – NLC

734
0
Ba Za Mu Yarda A Zaftare Albashin Ma’aikata Ba - NLC

Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, ta gargadi gwamnati da ma’aikatu game da dakatar da albashin ma’aikata ko kuma zaftare shi da sunan yaki da annobar Coronavirus.

Shugaban kungiyar Ayuba Wabba ya bayyana haka, a cikin wata sanarwa da ya fitar domin tunawa da ranar ma’aikata ta duniya.

Wabba ya yi kira kungiyar ta kowace jiha ta bijire wa duk wani yunkurin gwamnati da ma’aikatu na zaftare albashin ma’aikata, saboda a cewar sa ba yanzu ba ne lokacin rage albashi.

Ya ce su na tabbatar wa ma’aikata cewa babban abin da su ka sa gaba shi ne farfado da tattalin arziki su koma bakin aikin su, sannan sun maida hankali wajen inganta albashin ma’aikata tare da maida ma’aikatan da su ka rasa ayyukan su.

Sai dai Wabba ya ce duba da halin da ake ciki na annobar Coronavirus, bana ba za a gudanar da bikin tunawa da ranar ma’aikata kamar yadda aka saba ba.