Home Labaru Pochettino Ya Ce Neymar Na Da Sauran Dimbin Shekarun Kwallon Kafa

Pochettino Ya Ce Neymar Na Da Sauran Dimbin Shekarun Kwallon Kafa

9
0

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta PSG Mauricio Pochettino ya yi ikirarin cewa ko shakka babu dan wasan gaba na kungiyar Neymar Junior ya na da sauran shekarun nuna bajinta a duniyar kwallo sabanin ikirarin dan wasan da ke ganin zamanin sa na dab da shudewa.

Cikin makon da ya gabata ne Neymar dan Brazil ya bayyana cewa yana tunanin gasar cin kofin Duniya ta 2022 da za ta gudanar a Qatar ta zama karshen taka ledar sa a makamanciyar gasar ko kuma karshen nuna bajintar sa baki daya.

Neymar ya shaidawa manema labarai cewa, baya tunanin zai sake daukar shekaru a nan gaba yana kwallo.

Sai dai Pochettino ya alakanta kalaman na Neymar da tsantsar kankan da kai da ya ce dan wasan na da shi.

Acewar mai horarwar, Neymar mai shekaru 29 ya kan fadi kawai duk abin da ya zo ran sa idan ya na gaban manema labarai, amma dan wasan na da sauran karfi da kuma gagarumar gudunmawar bayarwa a duniyar kwallo.