Kotun sauraren karrakin zabe a jihar Kaduna, ta hana wani kwarare da jam’iyyar PDP ta gabatar wa kotu domin ya bada shaida a kan zabe saboda kurewar wa’adin gabatar da shaidu.
Shugaban kotun mai shari’a Ibrahim Bako, ya ce ba za a ba shaidar damar yin magana a kotun ba, saboda wa’addin kwanaki goma sha hudu da aka ba su na gabatar da shaidu ya wuce.
An dai gayyato kwarraren ne domin ya bada shaida a kan wasu kayayakin zabe da Hukumar Zabe ta yi amfani da su yayin zaben gwamna da aka yi ranar 9 ga watan Maris a jihar Kaduna.
Lauyoyin jam’iyyar APC da hukumar zabe sun ki amincewa da mai bada shaidar da jam’iyyar PDP da dan takarar ta Isah Ashiru su ka gabatarwa kotun.
Karanta Labaru Masu Alaka: Gwamnonin PDP Sun Fi Son Kayode Fayemi A Kan El-Rufa’i
Lauyoyin biyu sun shaida wa kotun cewa, an sanar da su cewa za a gabatar da mai bada shaidar ne daf da fara sauraren shari’ar, inda su ka ce su na bukatar lokaci domin yin nazarin da kuma shirya irin tambayoyin da za su yi wa mai bada shaidar, lmarin da ya sa su ka bukaci kotu ta hana shi bada shaidan.
Kotun ta dage ci-gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 15 ga watan Yuli domin sauraren shaidun APC da kuma Hukumar zabe.