Home Labaru INEC Ta Yi Magudi A Zaben Osun – Inji Alkali

INEC Ta Yi Magudi A Zaben Osun – Inji Alkali

418
0
Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta kasa, INEC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta kasa, INEC

Wani Alkalin Kotun Koli da bai amince da hukuncin da kotun ta yanke a kan zaben Gboyega Oyetola a matsayin gwamnan jihar Osun, ya zargi Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta ta kasa da tafka magudi a zaben.

Alkalan kotun biyu da su ka hada da Kumai Akaas da Paul Galinje sun ce ba su amince da hukuncin da aka zartar na tabbatar da nasarar Oyetola na jam’iyyar APC ba.

karanta Labaru Masu Alaka: INEC Ta Fara Shirin Daukar Ma’aikatan Wucin-Gadi

Mai shari’a Akaas ya zargi hukumar zabe da tafka magudi yayin zaben raba gardama da aka gudanar, yayin da mai shari’a Galinge ya ce ya dace kotu ta maida hankali a kan zargin magudin da aka ce an yi lokacin zaben raba gardamar.

Mista Akaas ya ce, hukumar zabe ta ba da wani kwakkwaran dalili na yin zaben raba gardama tun farko, ya na mai cewa kamata ya yi hukumar ta zama alkali ba ta nuna fifiko ba.

karanta Labaru Masu Alaka: INEC Za Ta Dauki Masu Yi Wa Kasa Hidima Da Su Ka Nuna Kwazo A Aikin Su

Ya ce tun lokacin da hukumar zaben ta ce zaben bai kammalu ba alama ce da ke nuna ta na shirya wata makarkashiya.