Majalisar dokoki ta kasa ta sha alwashin sa baki a lamarin ci-gaba da tsare Shugaban kungiyar Shi’a Ibraheem El-Zakzaky.
El-Zakzaky dai ya kasance a tsare tsawon watanni da dama bayan rikicin da ya barke tsakanin mabiyan sa da rundunar sojin Nijeriya.
Karanta Labaru Masu Alaka: ’Yan Shi’a Sun Karya Kofar Majalisar Tarayya
Shugaban masu rinjaye na majalisar Alhassan Doguwa, ya dauki alkawarin ne yayin da ya ke yi wa mabiya akidar shi’a da su ka gudanar da zanga-zanga jawabi a harabar majalisar da ke Abuja.
Karanta Labaru Masu Alaka: ‘Yan Shi’a Sun Gabatar Da Shaidar Cewa El-Zakzaky Ya Makance
Jagoran kungiyar masu zanga-zangar Abdullahi Musa ya yi zargin cewa, lafiyar shugaban su na kara tabarbarewa, kuma ya na bukatar kulawar gaugawa.
You must log in to post a comment.