Home Labaru PDP Ta Zargi Jonathan Da Matar Sa Da Yi Wa Jam’iyyar APC...

PDP Ta Zargi Jonathan Da Matar Sa Da Yi Wa Jam’iyyar APC Aiki

468
0
Goodluck Jonathan, Tsohon Sugaban Kasa
Goodluck Jonathan, Tsohon Sugaban Kasa

Jam’iyyar PDP reshen jihar Bayelsa, ta zargi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da matar sa Patience da rashin goyon bayan ta, ta hanyar bayyanawa da kuma bada gudummawar kudi yayin da zaben gwamnan jihar ke karatowa.

A cikin wata sanarwa da jami’in gudanarwa na jam’iyyar Isaac Ipidei ya fitar, ana zargin Jonathan da ganawa da Cif Timipre Sylva, wanda dan jam’iyyar APC ne.

Jam’iyyar PDP, ta ce ta yi wannan korafin ne a kan Jonathan, su ke zargin cewa ya na kokarin bata tafiyar jam’iyyar ne gabannin zuwan zaben gwamnan jihar. PDP dai ta yi korafin cewa Jonathan ba ya taimaka mata ta kowace hanya, kuma baya karfafa wa ‘yan siyasa gwiwa, musamman masu takarar kujerar gwamnan jihar.