Home Labaru Babu Wanda Ya Isa Ya Hana Mu Yin Zanga-Zanga A Abuja -‘Yan...

Babu Wanda Ya Isa Ya Hana Mu Yin Zanga-Zanga A Abuja -‘Yan Shi’a

518
0

Mabiya akidar Shi’a sun ce, dokar hana zanga-zanga a birnin Abuja ba ta dame su ballantana su yi la’akari da ita, tunda su ba ‘yan sanda ne su ka sa su yin zanga-zanga ba.

Daya daga cikin mabiya akidar Malam Bala Sufi ya bayyana wa manema labarai cewa, babu wanda ya isa ya hana su nema wa shugaban su ‘yanci, don haka za su cigaba da fitowa har Mahadi ya bayyana mutukar ba a saki Ibrahim El-Zakzaky ba.

Idan dai za a iya tunawa, a Alhamis da ta gabata ne aka yi shari’ar Ibrahim El-Zakzaky a babbar kotu da ke zama a Kaduna, inda a karshe alkalin kotun ya sake dage sauraron karar zuwa ranar 29 ga watan Yuli.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa, akwai yiwuwar Malamin ya iya rasa idon sa daya da ya rage matukar gwamnati ba ta sake shi ya je ya nemi magani ba.