Home Home PDP Ta Naɗa Sabon Shugaban Riƙo Na Ƙasa

PDP Ta Naɗa Sabon Shugaban Riƙo Na Ƙasa

189
0
Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP, ya amince da nadin Ambasada Umar Iliya Damagum a matsayin sabon shugaban riƙo na jam'iyyar na ƙasa.

Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP, ya amince da nadin Ambasada Umar Iliya Damagum a matsayin sabon shugaban riƙo na jam’iyyar na ƙasa.

A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar bayan ganawar gaugawa da kwamitin gudanarwar ta na ƙasa ya gudanar, PDP ta ce ta ɗauki matakin ne domin biyayya ga hukuncin babbar kotun jihar Benue.

A ranar Litinin da ta gabata ne, kotu ta haramta wa Ayu gabatar da kan sa a matsayin shugaba har sai ta saurari ƙarar da wasu ‘yan jam’iyyar su ka shigar.

Da ya ke ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron a helkwatar PDP ta ƙasa, sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar ya ce sun ɗauki matakin ne domin bin umarnin tsarin mulkin jam’iyyar. Debo Ologunagba, ya ce bayan nazari a kan hukuncin kotun da kuma la’akari da sashe na 45 (2) na tsarin mulkin PDP, kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya amince da naɗa mataimakin shugaban jam’iyyar mai kula da shiyyar arewa Ambasada Umar Ililya Damagum a matsayin sabon shugaban riƙo na jam’iyyar na kasa.

Leave a Reply