
Ƙungiyar Kishin Ƙabilar Yarabawa Zalla ta Afenifere, ta bayyana kakkausan furucin da Shugaban Majalisar Dattawan Ƙabilar Igbo Emmanuel Iwuanyanwu ya yi a kan Yarabawa da cewa, kalamai ne masu rura wutar raba kan jama’a da kuma cusa ƙiyayya a tsakanin ƙabilun biyu.
Iwuanyanwu wanda shugaban dattawan kabilar Ibo ta Ohaneaze Ndigbo ne, ya kira waɗanda su ka nuna wa ƙabilar Igbo tsana da tsangwama a lokacin zaɓen shekara ta 2023 a Legas cewa ‘yan jagaliyar siyasa ne.
Emmanuel Iwuanyanwu dai ya yi furucin ne a birnin Awka na Jihar Anambra, lokacin da ya ke jawabi a wajen taron murnar cikar Gwamnatin Charles Soludo shekara ɗaya a kan mulki.
Iwuanyanwu ya yi maganar ne matsayin raddin a kan taho-mu-gamar da aka riƙa gwabzawa tsakanin Yarabawa da kabilar Igbo ranar zaɓen gwamna a Legas, inda ya yi tir da rikicin ya kuma gargaɗi Yarabawa kada su sake tsokanar ƙabilar Igbo da rigima.
Sai dai Ƙungiyar yarbawa ta Afenifere ta maida ma shi raddi ta hannun Sakataren Shirye-shiryen ta Kole Omololu, inda ta ragargaji Iwuanyanwu, cewa su nisanci tashin hankali su rungumi zaman lafiya da kyakkyawar zamantakewa da sauran ƙabilu.
You must log in to post a comment.