Home Home Najeriya: Bashin Da Gwamnati Ta Ciyo Daga Bankunan Gida Ya Kai Naira...

Najeriya: Bashin Da Gwamnati Ta Ciyo Daga Bankunan Gida Ya Kai Naira Tiriliyan 28.43

56
0
Kudaden da bankuna ke ba gwamnatin tarayya ya karu da Naira tiriliyan 3 da biliyan 77 a cikin watanni biyu na farkon shekara ta 2023.

Kudaden da bankuna ke ba gwamnatin tarayya ya karu da Naira tiriliyan 3 da biliyan 77 a cikin watanni biyu na farkon shekara ta 2023.

Alkaluman da aka samu daga babban bankin Nijeriya sun nuna cewa, jimillar bashin da gwamnati ta samu ya tashi daga Naira tiriliyan 24 da biliyan 66 zuwa Naira tiriliyan 28 da biliyan 43 a karshen watan Fabrairun shekara ta 2023.

Bankin CBN ya bayyana a cikin rahoton sa na Kididdigar Kudi da Lamuni cewa, bashin ya tashi daga Naira tiriliyan 14 da biliyan 900 a karshen watan Janairun shekara ta 2022 zuwa Naira triliyan 26da biliyan 65 a shekara ta 2023.

A cikin wata sanarwa da bankin CBN ya fitar, wani dan kwamitin kula da harkokin kudi Aliyu Sanusi, ya ce ana bukatar tsaurara matakan takaita yawan bashin ne domin daidaita illolin kashe kudade da su ka shafi zabe da yadda ake kashe kudaden da gwamnati ke son karbar rance a cikin kasa ta 2023.

Ya ce manyan abubuwa da ke kunshe a yarjejeniyar sirri ta su ne girman bashi a kan gwamnati, wanda ya karu da sama da kashi 78 cikin 100 a watan Disamba na shekara ta 2022, wanda hakan ya biyo bayan lamunin da Gwamnatin Tarayya ta samu daga bankin CBN.

Leave a Reply