Home Labaru Pandora Papers: Nijeriya Ta Fara Daukar Mataki A Kan Wadanda Aka Ambata

Pandora Papers: Nijeriya Ta Fara Daukar Mataki A Kan Wadanda Aka Ambata

67
0

Hukumar kula da da’ar ma’aikata, ta bayyana kokarin da ta ke yi na binciken jami’an gwamnati na baya da na yanzu, wadanda ake zargi da mallakar kaddarori ba bisa ka’ida ba.

Shugaban Hukumar Farfesa Mohammad Isah, ya ja hankalin jama’a da ma’aikatan gwamnati zuwa ga aikin tantance kaddaorin su, inda ya ce an fara daukar matakai a kan ‘yan Nijeriya da binciken Pandora Papers ya bankado sun mallaki kaddarori da kudadde haram a kasashen waje

Farfesan ya kara da cewa, hukumar ta na aiki tare da kungiyoyi masu zaman kan su, wadanda da su aka yi aikin bankado mutanen da ake zargi, kuma akwai sauran jami’an gwamnati da ake kokarin neman Karin bayani a kan rawar da su ka taka a binciken Pandora Papers.

Ya ce su na daukar sabbin matakan tabbatar da masu rike da mukaman gwamnati da na siyasa sun bi kaidojin da ya kamata wajen bayyana kadarorin da su ka mallaka, kuma dole ne kowane ma’aikaci ya bayyana abin da ya mallaka.