Home Labaru Kotu Ta Hana Kwasar Dala Miliyan 418 A Biya Dillalan Gada-Gada

Kotu Ta Hana Kwasar Dala Miliyan 418 A Biya Dillalan Gada-Gada

61
0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta dakatar da Gwamnatin Tarayya kwasar dala miliyan 418 daga asusun jihohi 36 da ƙananan hukumomi 774, da nufin biyan wasu dillalan gada-gada da ke iƙirarin sun yi wa jihohi da ƙananan hukumomi ayyukan adadin kuɗaɗen a shekarun baya.

Dillalan dai sun ce, sun yi wa jihohi da ƙananan hukumomi aikin tuntuɓa ne da wasu kwangiloli tsakanin shekara ta 1995 da 2002, wajen ƙoƙarin aikin dawo masu da kuɗaɗen da aka riƙa ɗibar masu ana biyan bashin Paris Club da London Club.

Babban Mai Shari’a Iyan Ekwo ya umarci Gwamnatin Tarayya ta dakatar da fara kwasar kuɗaɗen da ta shirya farawa daga watan Nuwamba, har sai bayan an kammala shari’ar da Gwamnonin su ka shigar a gaban sa.

Gwamnonin dai sun shigar da ƙarar ne ta hannun gogaggun lauyoyin su biyu, wadanda su ka hada da Jibrin Okutedo da Ahmed Raji.

Lauyoyin sun ce, masu iƙirarin sai an biya su kuɗaɗen har dala miliyan 418 ‘yan gada-gada ne babu gaskiya a lamarin su.