Home Labaru Naira Biliyan N100 Ba Za Su Isa A Gudanar Da Shi Ba

Naira Biliyan N100 Ba Za Su Isa A Gudanar Da Shi Ba

115
0

Shugaban hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce naira biliyan 100 da aka ware domin gudanar da zaben shekara ta 2023 a kasafin shekara ta 2022 ba zai ishe su ba ko kadan.

Farfesan ya bayyan haka ne, lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin zabe na majalisar dattawa domin kare kasafin kudin hukumar na shekara ta 2022.

Ya ce yayin da aka ware wa babban zaben shekara ta 2019 naira biliyan 189, babu ta yadda za a yi na shekara ra 2023 ya zama naira biliyan 100 kadai.

Farfesa Yakubu, ya ce za su bukaci karin kudi saboda sun fadada rumfunan zabe, kuma za su gabatar da sabbin fasahohi domin zabe da sauran su.

Leave a Reply