Home Labaru Osinbajo Ya Ce Dole Ne Jihohi Su Habaka Hanyoyin Samun Su Na...

Osinbajo Ya Ce Dole Ne Jihohi Su Habaka Hanyoyin Samun Su Na Cikin Gida

14
0
Osinbajo Ya Ce Rashawa Ce Ta Haddasa Matsanancin Talauci A Nijeriya
Osinbajo Ya Ce Rashawa Ce Ta Haddasa Matsanancin Talauci A Nijeriya

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi kira ga jihohin Najeriya su sake nazari mai zurfi, su kuma yi Tunani kamar kasashe masu ‘yancin cin gashin kai, ta yadda za su bunkasa samun kudaden shiga na cikin gida domin tafiyar da lamurran su.

Yemi Osinbajo ya yi wannan tsokaci ne a taron farko na dandalin saka hannun jari na jihar Ekiti da ya gudana a birnin Ado-Ekiti.

A cewar sa, kamata yayi gwamnonin jihohi su fara tunani na daban, a maimakon dogara da abinda suke samu daga gwamnatin tarayya, akwai bukatar su yi tunani kamar kasa mai cikakken iko don bunkasa hanyoyin samun kudadden shiga da zai taimaka wajen raya jihohin su.

Mataimakin shugaban kasar ya jaddada cewa wasu jihohin na da hanyoyin samun kudaden shiga na cikin gida masu kyau.

Haka kuma, Osinbajo ya ce wajibi ne jihohi su dauki nauyin wasu hakkokin da ke rataye a kan su, kamar biyan albashi daga kudaden shiga na cikin gida da su ke samu, wanda kuma zai rage musu dogaro kacokam kan gwamnatin tarayya.