Home Labaru Kungiyar Dattawan Arewa Ta Mai Da Martani Ga ‘Yan Naija-Delta

Kungiyar Dattawan Arewa Ta Mai Da Martani Ga ‘Yan Naija-Delta

26
0

Kungiyar dattawan Arewa ta sake gargadi ga masu da’awar cewa ya zama tilas mulkin Najeriya ya koma kudu a shekara ta 2023, wanda a wannan karon, tana maida martani ne ga kungiyar ‘yan yankin Neja-Delta.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta ‘yan yankin Neja-Delta, ta yi barazanar cewa dole ne yankin Arewa da yanzu haka ke mulki, ya jira har zuwa shekarar 2031, wato bayan shekaru 10 kenan, kafin ya sake samar da wani shugaban kasa.

Sanarwar wadda sakataren yada labaran kungiyar ta ‘yan yankin Naija-Delta na kasa, Ken Robinson ya fitar a birnin Fatakwal, ta ce bai kamata Arewa ta yi tunanin yin wani shugaban kasa ba bayan karshen wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari na.

To sai dai kungiyar dattawan Arewa ta jaddada matsayar ta akan wannan cece-kuce, na cewa yankin ba zai lamince wa duk wata barazana kan shugabancin kasa ba, ta na mai cewa yin barazana kan lamarin ba zai haifar da da mai ido ba.

Dakta Hakeem Baba Ahmed, wanda shi ne daraktan yada labarai da tallafawa na kungiyar dattawan Arewa, ya yi gargadin cewa akwai yiyuwar kungiyar PANDEF da sauran kungiyoyi daga kudanci ba su saurari matsayar Arewa ba kan lamarin a can baya, da ta bayyana cewa ba za’a yi mata barazana ko tsoratarwa daga wata kungiya ko yanki ba kan batun zaben shekarar 2023 ba.