Home Labaru Oshiomhole Ya Jinjinawa Buhari Bisa Rage Kudin Man Fetur

Oshiomhole Ya Jinjinawa Buhari Bisa Rage Kudin Man Fetur

306
0
Oshiomhole Ya Jinjinawa Buhari Bisa Rage Kudin Man Fetur
Oshiomhole Ya Jinjinawa Buhari Bisa Rage Kudin Man Fetur

Shugaban jam’iyyar APC ta kasa Adams Oshiomhole ya jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan amincewa da rage farashin man fetur daga naira 145 zuwa naira 125.

Bayanin haka na kunshe ne a cikin wata takarda da babban sakataren yada labaran sa Simon Ebegbulem ya fitar a Abuja, inda ya kwatanta hukuncin da Buhari ya yi na rage farashin man da shugabanci na gari da kuma jin kai ga al’ummar Nijeriya.

Takardar ta kara da cewa, a madadin kwamitin ayyuka na jam’iyyar su na jinjinawa shugaban kasa Buhari bisa rage farashin kudin man fetur da ya yi.

Haka kuma, Oshiomhole ya ce, gwamnatin Buhari ta tabbatar wa da duniya cewa ta na jin tausayin al’ummar ta, musamman ta hanyar ganin ta saukaka musu rayuwa ta kowanne fanni, a dai-dai lokacin da tattalin arzikin duniya ke cigaba da fuskantar barazana sakamakon bullar cutar Corona.

Idan dai ba a manta ba, a ranar Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a rage farashin litar man fetur zuwa naira 125, sabani yadda ya ke ada a kan farashin naira 145.